El-Zakzaky na shirin neman magani a wata kasa bayan Indiya

El-Zakzaky na shirin neman magani a wata kasa bayan Indiya

Kamar yadda rahotanni suka zo, sun nuna cewa Shugaban kungiyar Islamin Movement in Najeria (IMN), wacce aka fi sani da kungiyar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky na a hanyarsa ta dawowa daga kasar Indiya inda ya je yin magani sakamakon rashin yarda da tsarin yi masa magani a asibitin New Delhi.

Sai dai kuma Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa El-Zakzaky ya so zullewa ne ta amfani da damar da kotu ta ba shi na zuwa Indiya.

A sanarwa daga babban sakatariyar ma'aikatar labarai Grace Isu Gekpe ta ce tun isar jirgin daular larabawa, Elzakzaky ya nemi amshe Fasfo din sa inda kuma bayan isa Indiya ya so sauka a babban otel da kuma samun damar ganawa da jama'ar da ya ga dama.

Hana El-Zakzaky samun wannan bukata ya sanya shi kin wani likita ya duba shi da kuma fitar da sakon sauti na nuna ya na cikin mafi munin hali.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sheikh El-Zakzaky zai dawo gida Najeriya

Gwamnatin ta ce Indiya ta hana El-Zakzaky amfani da kasar ta wajen fadada harkar kungiyar sa ta IMN zuwa ta duniya.

Sai dai kuma babban almajirin El-Zakzaky, Muhammad Ibrahim Gamawa ya ce za su nemi tafiya wata kasar cikin zabin Malasiya, Indunsiya ko kuma Turkiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel