Bayan shafe shekaru ba a ji duriyarta ba, jaruma Kubura Dako ta bayyana cikin wani yanayi a wani hoto

Bayan shafe shekaru ba a ji duriyarta ba, jaruma Kubura Dako ta bayyana cikin wani yanayi a wani hoto

- Bayan ta shafe shekaru masu yawan gaske ba a sake jin duriyarta ba, tsohuwar jaruma Kubrah Dako ta bayyana cikin wani yanayi

- Jarumar ta bayyana cikin wani hoto da ya bar alamar tambaya a zukatan mutane da yawa da suka sanya idonsu a kan hoton

- Kwanakin baya dai an bayyana cewa jarumar ta tafi kasar Malesiya domin cigaba da karatun ta na jami'a

Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood Kubrah Dako, bayan shafe shekaru masu yawan gaske da ta yi ba a sake jin duriyarta ba, kuma ba a sake ganinta a cikin fim din Hausa ba, kwatsam sai ganin wani hotonta akayi yana yawo a shafukan sada zumunta.

Hoton tsohuwar jarumar dai ya bayyana yayin da aka nunata cikin wani yanayi marar kyaun gani, saboda irin suturar da ta sanya ya bar ayar tambaya da yawa a zukatan jama'a, saboda kwata-kwata kayan basu yi kama dana Hausawa ba.

KU KARANTA: Sarki mai adalci: Sarki Sunusi yayi abin da babu wani Sarki da ya taba yi a fadin Najeriya

Idan ba a manta ba, tsohuwar fitacciyar jarumar Kubrah Dako, ta daina fitowa a cikin wasan fina-finan Hausa tsawon wasu shekaru, inda daga baya kuma muka samu labarin cewa tana karatu a kasar Malesiya.

Tun daga labarin karatunta a kasar Malesiya dai ba a sake jin duriyarta ba sai wannan 'yan kwanakin inda ta bayyana sanye da wadannan kaya na jikin hoton. Allah dai ya kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel