Ganduje ya rabawa Alhazan Kano naira dubu biyar-biyar

Ganduje ya rabawa Alhazan Kano naira dubu biyar-biyar

Bayan kammala aikin hajjin bana, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da kyautar naira dubu biyar-biyar ga kowane daya daga cikin Alhazan Kano 3,170 dake kasa mai tsarki.

Babban sakataren hukumar jin dadin alhazai na jihar Kano, Muhammad Abba Danbatta, shi ne ya bayar da shaidar wannan tagomashi da Yammacin ranar Laraba cikin birnin Makkah.

Danbatta ya yiwa Alhazan Kano wannan albishir da cewar za su karbi tukwicinsu a cibiyoyin rukunan Alhazai daban-daban da aka tanada domin tabbatar da jin dadinsu a birnin Makkah.

Ya yi bayanin cewa, gwamna Ganduje ya yiwa Alhazan Kano wannan kyauta a matsayin wani babban goro inda yake sa ran za su ramawa kura kyakkyawar aniyarta da addu'o'i.

A yayin da ake sa ran dawowar Alhazai gida Najeriya, babban jami'in hukumar mai kula da jin dadin Alhazai, ya kuma gargade su a kan kiyaye duk wasu dokoki da aka gindaya musamman nesanta kawunansu daga duk wasu haramtattun ababe.

KARANTA KUMA: Sheikh Nasiruddeen Funtua ya rasu a kasar Saudiya

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, a ranar Alhamis ya dawo Najeriya daga kasa mai tsarki bayan sauke farali na aikin hajji a bana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel