Sheikh Nasiruddeen Funtua ya rasu a kasar Saudiya

Sheikh Nasiruddeen Funtua ya rasu a kasar Saudiya

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu daga jaridar Katsina Post sun ruwaito cewa, wani mashahurin malamin addinin Islama dan jihar Katsina, Sheikh Nasiruddeen Adam Funtua, ya riga mu gidan gaskiya a kasa mai tsarki kwanaki kalilan bayan kammala aikin hajjinsa a bana.

Duk da cewar an samu karancin bayanai dangane da rasuwar fitaccen malamin yayin tattara wannan rahoto, mun samu cewa mutuwa mai yankan kauna ta tari hanzarin sa tun da safiyar ranar Alhamis.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da jana'izar marigayi Sheikh Funtua a birnin Makkah.

Sheikh Funtua yayin rayuwar sa ya shahara wajen jagorantar yada ayyukan da'awa a kafofin watsa labarai na gidajen radiyo da kuma na talabijin daban-daban a birnin na Katsinan Dikko.

Manema labarai sun tabbatar da cewa, Sheikh Funtua ya kasance daya daga cikin Alhazan jihar Katsina uku da suka riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiya yayin aikin hajjin na bana inda wasu Mata biyu su rigaye shi.

KARANTA KUMA: Sanata Ahmed Lawan ya dawo daga aikin Hajji

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya aikewa da Alhazan jihar sa 3,170 da ke kasa mai tsarki kyautar naira dubu biyar-biyar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel