Kannywood: Adam Zango ya yi martani akan kamun jarumi Sanusi Oscar

Kannywood: Adam Zango ya yi martani akan kamun jarumi Sanusi Oscar

Fitaccen jarumin nan na Kannywood, Adam A. Zango ya yi martani akan kamun jarumi Sanusi Oscar da jami’an tsaro suka yi a jihar Kano.

Adam Zango ya bayyana cewa a yanzu Sanusi ya sake samun sabuwar ilimi, inda ya karfafa masa gwiwa akan cewa komai mai wucewa ne.

Har ila yau Zango ya bayyana cewa kamar yadda yake bayar da laarin shiga gidan yari a yanzu, wata rana shima Oscar zai bayar don haka yayi hakuri.

Zango ya wallafa hakan ne a shafinsa na Instagram inda yace: “KA SAKE SAMUN SABUWAR ILIMI. @sunusi_oscar__442 .

“Kayi hakuri dan uwa babu abinda baya wucewa. Wata rana yadda nake bada labarin shiga gida yari, kaimu haka zaka bada.”

Daga karshe jarumin ya bayyana bakin ciki, hassada, kyashi da munafurci a matsayin taken Kannywood.

KU KARANTA KUMA: JAMB ta ba Attahiru Jega mukami, zai shugabanci kwamitin daukar dalibai a jami’a

Yace: “Bakin ciki, kyashi, hassada, munafurci.......wadan nan sune national anthem din KANNYWOOD!”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel