Sojoji sun yi maganin wasu ‘Yan Boko Haram a Garin Kollarum

Sojoji sun yi maganin wasu ‘Yan Boko Haram a Garin Kollarum

Mun samu labari cewa dakarun sojojin saman Najeriya na Operation LAFIYA DOLE sun yi maganin wasu ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka addabi Najeriya da yankin Yammacin Afrika.

Sojojin saman kasar sun bayyana cewa Dakarunsu sun kai wasu hare-hare a kan Mayakan Boko Haram a Kollarum. Kollarum wani karamin Kauye ne da ke daf da tafkin Chad a jihar Borno.

“An kai wadannan hare-hare ne a Ranar 9 ga Watan Agusta a shirin GREEN SWEEP 3 inda a ka dumfari wasu gidaje uku a wannan Kauye bayan mun samu labarin cewa Mayakan Boko Haram su na yankin.”

Sojojin sun kuma bayyana cewa:

KU KARANTA: Dakarun Najeriya sun kafa cibiyar sa-ido a daf da Sallah a Filato

“Bayan bincike na musamman na ISR ya nuna cewa akwai wasu Mayakan Boko Haram dankare a wannan yankuna, sai Dakaru su ka shiga da jiragen yaki uku na Alpha Jet domin far ma wuraren.”

“Luguden wutan da jiragen su ka yi, ya rutsa da ‘yan ta’addan a inda a ka yi hari, inda a ka yi masu mugun ta’adi sannan a ka rusa gidajensu. Inji mai magana da bakin Sojojin saman kasar.

A wannan jawabi, jami’in sojan ya kara da cewa za su cigaba da kokarin ganin sun yi maganin kaf Mayakan ta’addan Boko Haram da ke addabar Bayin Allah a yankin Arewa maso Gabashin kasar

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel