Sanata Danmusa ya gargadi Buhari a kan kisan da 'yan bindiga ke yi a Jihar Katsina

Sanata Danmusa ya gargadi Buhari a kan kisan da 'yan bindiga ke yi a Jihar Katsina

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Mamman Abubakar Dan Musa, ya yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya shiga cikin batun kisan jama'ar jiharsa da 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda ke yi kafin al'amura su kara tabarbarewa.

Da yake magana da manema labarai a gidansa ranar Laraba, Danmusa ya ce lamarin tsaro ya tababare a jihar Katsina, musamman a kananan hukumomin Batsari, Safana da Danmusa, inda ya ce kullum sai an kai hare-hare.

Ya kara da cewa jami'an tsaro sun kasa shawo kan lamarin.

"Buhari ya san waye Mamman sarai ma kuwa, kuma ya san ni dan gwawarmayar tabbatar da adalci ne da ba ya maganar banza. A shekarar 1960, na jagoranci zanga-zanga a lokacin da nake dalibi a makarantar horon malamai ta Katsina domin yakar rashin adalci da rashin tausayi, a saboda haka babu abinda zai sa yanzu naga tsaro yana lalacewa a jiha ta kuma nayi shiru da bakina.

"Ku 'yan jarida kun san cewa gwamnonin sun yi arewa a farkon watannan, inda suka bayyana cewa sun yi yafiya gaa 'yan bindiga, kuma kowa ya san suna nufin 'yan bindiga masu makami da ke kashe jama'a.

"Kwanaki kadan da bayyana hakan, amma har yanzu baku ji labarin wani dan bindiga ya fito ya ajiye makamansa ba, lamarin ma sai kara tabarbarewa ya yi," a cewar Sanata Danmusa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel