Wani soja da aka kora a aiki saboda ya harbi shugabanshi, an sake cafke shi da laifin fashi da makami a jihar Kaduna

Wani soja da aka kora a aiki saboda ya harbi shugabanshi, an sake cafke shi da laifin fashi da makami a jihar Kaduna

- An kama wani tsohon soja da aka kora daga aiki a shekarar 2006 bayan ya harbi Kwamandanshi da laifin fashi da makami

- An kama sojan a jihar Kaduna yayin da yaje yayi fashi a unguwar Malali dake cikin kwaryar jihar

- Sojan ya bayyana cewa a shirye yake ya karbi kowanne irin hukunci hukuma ta yanke a kanshi, kuma zai canja halinshi nan ba da dadewa ba

Wani soja da aka kora a aiki mai suna Lance Corporal Khalid Mohammed, an bayyana shi jiya Laraba tare da wasu mutane 78 da rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama da laifin fashi da makami.

Sojan ya bayyana cewa yana yin wannan sana'a ta fashi da makami tun shekarar 2006 bayan an koreshi daga aikin soja dalilin harbin wani Kwamandanshi da yayi.

KU KARANTA: Wata budurwa 'yar Najeriya ta ajiye aikin da ake biyanta naira miliyan 22, saboda tana so ta bude nata kasuwancin

Sojan mai 'ya'ya guda biyu, an kama shi da laifin fashi da makami a unguwar Malali dake jihar Kaduna, yayi alkawarin canja rayuwarshi bayan an kama shi sannan kuma ya bayyana cewa a shirye yake ya karbi kowanne irin hukunci da aka yanke masa, saboda shi ya san cewa ya cancanta da kowanne irin hukunci aka yi masa.

Ko mene yasa aka fiya samun jami'an tsaron kasar nan da hannu wajen aikata ayyukan ta'addanci a kasar nan?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel