Gwamnan jihar Bauchi ya ba wanda Buhari ya kora mukamin Kwamishina

Gwamnan jihar Bauchi ya ba wanda Buhari ya kora mukamin Kwamishina

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ba Ladan Salihu, tsohon Shugaban gidan radiyon tarayya wato FRCN, wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kora a shekarar 2016 mukamin kwamishina.

An salami Ladan ne dai bayan samunsa da hannu dumu-dumu cikin harkallar cuwa-cuwa da sama da fadi akan wasu kudade.

Shi ma gwamnan har zuwa ranar da aka rantsar da shi, ya na fuskantar tuhuma a kotu bisa zargin karkatar da makudan kudade a lokacin da ya na Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An dakatar da shari’ar da ake tuhumar Bala ce, sakamakon rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi. A dokar Najeriya dai gwamna ya na da kariya, don haka ba za a gurfanar da shi kotu ba, har sai bayan ya kammala wa’adin sa.

Bala ya mika sunayen kwamishinonin sa ga ‘yan majalisar da ake tafka kwatagwangwamar yadda aka yi zaben shugabannin su. Ya mika sunayen ne ranar Alhamis da ta gabata.

Cikin wadanda ya mika sunayen na su, har da tsohon na hammnun daman Shugaban Buhari, wanda tuni ya dawo daga tafiyar shugaban kasar wato Aliyu Tilde.

Shi kuwa Ladan Salihu, bayan korar sa da Buhari ya yi daga FRCN a cikin 2016, sai ya nemi takarar zama sanatan Bauchi, amma bai yi nasara ba.

KU KARANTA KUMA: Sowore bai da ikon da zai kira zanga-zangar juyin juya hali - Oshiomhole

Daga nan kuma sai ya bi zugar siyasar Bala Mohammed, ya zama daraktan yada labarai na kamfen din Bala a takarar neman gwamnan jihar Bauchi. Sun yi nasara, guguwar Bala ta kayar da gwamana Mohammed Abubakar na APC a zaben 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel