Hajjin Bana: Bamu karbi kudin hadayar maniyyatan Kano ba - Hukumar Alhazai
A yayin da hadaya wato yanka dabba ta kasance wani rukuni cikin hukunce-hukunce na cikar ibadar aikin Hajji, wani al'amari ya taso a kanta tsakanin hukumar jin dadin Alhazai da maniyyatan jihar Kano.
Hukumar jin dadin Alhazai reshen jihar Kano, ta musanta karbar kudin hadayar maniyyatan jihar da za su sauke farali wajen gudanar da aikin Hajji na bana a kasar Saudiya.
Babban sakataren hukumar, Muhammad Abba Danbatta, shi ne ya shaidawa manema labarai wannan rahoto a birnin aminci na Madinatun Munawwara dake kasa mai tsarki. Ya ce babu ko asi na wani maniyyacin Kano da hukumar ta karbi kudin hadayarsa.
Jaridar Kano Today ta ruwaito cewa, Alhaji Danbatta ya yi wannan furuci domin mayar da martani a kan yadda wasu kungiyoyin masu zaman kansu ke ikirarin cewa hukumar Alhazan Kano tuni ta karbe kudin hadayar maniyyatan jihar, inda kuwa yace sam wannan al'amari bai tabbata ba.
KARANTA KUMA: Dalibin jami'ar kimiya da fasaha ya kashe Almajiri a Kano
A ranar Litinin 6 ga watan Agustan 2019, hukumar jin dadin Alhazai ta kasa NAHCON, ta kammala jigilar maniyyata 44,450 daga jihohin Najeriya 32 zuwa kasa mai tsarki. A ranar 3 ga watan Agustan ne hukumar ta kammala jigilar maniyyatan Kano 3,270 zuwa kasar Saudiya.
A karshen wannan mako ne dai ake shirin gudanar da bikin babbar Sallah, sai dai kasuwa ta yi kasa a yayin da farashin dabbobi yayi tashin doron zabuwa a wasu jihohin Najeriya kamar Kebbi, Kano da Oyo, sabanin yadda ta kasance a bara.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng