Mabanbanatan mutanen da a ke da su ya sa mulki ya ke da wahala – IBB

Mabanbanatan mutanen da a ke da su ya sa mulki ya ke da wahala – IBB

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana ire-iren mabanbantan mutanen da a ka tara a matsayin abin da ya sa shugabancin kasar nan ya ke da wahala.

Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya shugabanci kasar a lokacin mulkin soji, ya nuna cewa banbancin mutanen da a ke da su a Najeriya ya na da amfani domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Babangida wanda a ka fi sani da IBB ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai wahalar shugabanci ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu.

Honarabul Ndudi Elumelu da wasu ‘yan majalisar tarayya sun kai wa tsohon shugaban kasar ziyara ne a gidansa da ke Garin Minna, a cikin Jihar Neja inda IBB ya ba su wasu shawarwari.

KU KARANTA: An bayyana lokacin da Buhari zai rantsar da sababbin Ministoci

Janar Babangida ya fadawa Elumelu da Tawagarsa cewa ka da su sake yawan banbancin da a ke da shi a Najeriya ya ba su tsoro, sai da ma ya ce su nemi ganin yadda hakan zai amfane su.

Dattijon ya kuma nemi ‘yan majalisar su guji kaucewa tafarkin da Magabatan kasar su ka bi wajen hada kan al’umma. Babangida ya kuma yabawa da aikin manyan ‘yan majalisar adawar.

Janar Ibrahim Babangida ya fadawa ‘yan majalisar cewa lokaci ya yi da za su tsaya su yi wa mutanen Najeriya aiki domin ceto kasar. IBB ya ce an gama tirka-tirkar siyasa a halin yanzu.

Hon. Elumelu ya bayyana cewa sun zo har gida su gaida tsohon shugaban kasar ne domin su gode masa a kan kokarin da ya yi wajen samun mukamin da ya yi, inda ya kuma yi masa addu’o’i.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng