Gwamnan Jihar Yobe ya tafi kasar Saudi domin aikin Hajji

Gwamnan Jihar Yobe ya tafi kasar Saudi domin aikin Hajji

Mun samu labari cewa Mai girma gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya bar Najeriya zuwa kasa mai-tsarki watau Saudi Arabiya domin ya yi aikin hajjin wannan shekarar.

Darekta Janar na ofishin harkokin yada labarai na jihar Yobe, Malam Abdullahi Bego, shi ne wanda ya bada wannan sanarwa a wani jawabi da ya fitar a jihar a cikin farkon wannan makon.

Abdullahi Bego ya bayyana cewa gwamnan ya tafi wannan ibada mai girma ne tare da wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya 2 na jihar Lawan Shettima Ali da kuma Tijjani Zanna Zakariya.

Haka zalika a cikin tawagar gwamnan akwai mataimakin shugaban majalisar dokoki na jihar Yobe, Muhammad Auwal Isa, da kuma Ma’ajin jam’iyyar APC na jihar, Mohammed Gadaka.

KU KARANTA: Gwamnan Yobe ya rabawa marasa karfi abincin bikin sallah

Bego ya bayyana cewa gwamnan zai dawo gida ne a Ranar 14 ga Watan Agustan 2019 bayan kammala aikin hajjin wannan shekara. Hakan na nufin gwamnan zai yi sallah a kasa mai tsarki.

A jawabin da Darektan yada labaran ya fitar, bai bayyana wanda zai zama gwamnan rikon-kwarya kafin Mai girma Mala Buni ya dawo ba. Gwamnan zai shafe mako guda ne a kasar Saudiyya.

Kafin nan kun ji labari cewa gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello zai yi aikin hajji a wannan shekara. Haka zalika shugabannin majalisa; Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamilla su na Saudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel