Rauni: Babu Messi kungiyar Barcelona za ta buga wasan farko a kakar La Liga ta bana

Rauni: Babu Messi kungiyar Barcelona za ta buga wasan farko a kakar La Liga ta bana

Akwai yiwuwar kungiyar kwallon ta Barcelona za ta fara buga wasan farko na gasar La Liga a bana ba tare da haskaka kyaftin din ta ba, Lionel Messi, a sakamakon rauni da ya samu a kafarsa ta dama.

Bayan gudanar da bincike a kan raunin, kwararrun likitoci na kungiyar Barcelona sun ce Messi zai shafe akalla makonni biyu gabanin murmurewa. Messi ya samu raunin ne a yayin motsa jiki a ranar Litinin.

Tuni dai kungiyar Barcelona ta ce babu Messi za ta fafata a wasan sada zumunta na ranar Laraba da za ta buga a tsakanin ta da kungiyar kwallon kafa ta Napoli a birnin Miami na kasar Amurka.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta za ta fara buga wasan ta farko a kakar La Liga ta bana a ranar 16 ga watan Agusta. Za ta fafata wasan farko tsakaninta da kungiyar Atheltic Bilbao wadda za ta karbin bakuncinta a kasar Andalus wato Spain.

KARANTA KUMA: Hajjin Bana: NAHCON ta kammala jigilar maniyyata 44,450 zuwa kasar Saudiya

A wani rahoton na daban, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta sayar da dan wasan bayanta, Lauren Koscielny ga kungiyar Bordeaux ta kasar Faransa a kan fan miliyan 4.6.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel