Mai karatun Digirin PhD a Ilorin ya kirkiro maganin cutar tarin tibi

Mai karatun Digirin PhD a Ilorin ya kirkiro maganin cutar tarin tibi

Wani Bawan Allah da ke karatun Digirinsa na uku a fannin kimiyyar ilmin sinadarai a jami’ar tarayya da ke Ilorinya kirkiro wani magani da zai yaki cutar nan ta tarin tibi mai matsawa huhu.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Misitura Arowona, wanda ya ke binciken Digir-digir dinsa a karkashin Farfesa Joshua Obaleye, shi ne ya yi wannan namijin aiki da zai taimaki al’umma.

Misitura Arowona, a binciken na sa, ya yi aiki da wasu sinadari da za su inganta karfin sauran magungunan cutar tibi da a ka saba amfani da su, kamar yadda mujallar jami’ar ta Ilorin ta buga.

Yanzu haka Najeriya ta na cikin kasashen da ke fama da cutar tarin. Alkaluma sun nuna cewa Najeriya na sahun kasashe 30 da a ke yaki da cutar na tibi da HIV mai rusa garkuwar mutum.

KU KARANTA: Masana sun ce an kusa gano maganin hana mutuwa da kansa

Farfesa Joshua Obaleye wanda ya ke duba aikin wannan ‘Dalibi kwararre ne a wannan harkar wanda har ya taba rike shugaban sashen kimiyya na jami’ar inda yanzu ke aiki a kasashen waje.

Wannan Shehin Malami da Arowona ya ke Digirin sa uku watau PhD a hannunsa, ya na kuma koyarwa a babbar jami’ar nan ta Maharaja Sayajirao da ke cikin garin Vadodara a kasar Indiya.

Daga cikin sinadaran da Misitura Arowona ya yi amfani da su akwai ion, cobalt, copper da kuma zinc. Duk shekara fiye da mutane 407, 000 su ke kamuwa da wannan cuta ta tibi a cikin Najeriya.

Magungunan da a ka saba amfani da su ba su wuce; ciprofloxacin HCl, ofloxacin, pyrazinamide da moxifloxacin HCl. Duk cikin wadannan maganguna babu mai amfani da wadancan sinadarai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel