Ko me yayi zafi haka: An dakatar da fitaccen dan wasa Messi daga buga kwallo a duniya

Ko me yayi zafi haka: An dakatar da fitaccen dan wasa Messi daga buga kwallo a duniya

- An dakatar da kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Argentina Lionel Messi daga buga kwallo

- An dakatar da dan wasan ne na tsawon watanni uku, bayan yayi korafi cewa gasar kwallon kafa ta Copa America gurbatacciya ce

- An kuma bai wa dan wasan jan kanti a wani wasa da kasar ta Argentina ta buga da kasar Chile

Lionel Messi dan wasan da ke da shekaru 32 a duniya ya karbi jan kati a wani wasa da kasarsa ta Argentina ta buga da kasar Chile, inda kasar Argentina din ta lashe wasan da ci 2 - 1.

Dan wasan daga baya yayi korafin cewa anyi murdiya a wasan domin ana so kasar Brazil ta lashe wasan.

Kungiyar kwallon kafa ta yankin nahiyar Afirka ta kudu Conmebol ta ci dan wasan tarar dalar Amurka dubu hamsin. Sai dai kuma an ce dan wasan yana da damar da zai iya daukaka kara zuwa gaba daga nan zuwa kwanaki bakwai.

KU KARANTA: Bayan watanni biyar da haduwa a Twitter, saurayi da budurwa sun gama shiri tsaf domin angwancewa

Wannan mataki da kungiyar kwallon kafar ta dauka na nufin cewa dan wasan ba zai samu damar bugawa kasar sa wasannin da zata yi da kasashen, Jamus, Mexico da Chile ba a cikin wannan watan na Satumba da Oktoba masu zuwa.

Kasar ta Argentina dai za ta fara buga wasannin shiga cin gasar kofin duniya na shekarar 2022 a watan Maris na shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel