Babban bako: Sarki Salman ya gayyaci wani tsoho mai shekara 130 domin ya yi aikin hajji
Mutumin kasar Indonisiya mafi tsufa, Hajji OPhi Aydarous Samri, ya kasance mai kula da tsarkakan masallatai biyu a matsayin babban bakon Sark Salman a Hajjin bana.
Sarkin ya gayyaci Samri da iyalansa shida domin yin aikin Hajji a matsayin bakinsa cikin shirin karban baki na Hajji da Umrah, jaridun kasar suka ruwaito a ranar Laraba.
Jakadan kasar Saudiyya a Indonisiya, Essam Al-Thaqafi, ya ga Hajji Ohi Aydarous Samri da iyalansa a filin jirgin sama a ranar Talata kafin su tashi zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah.
A kowani shekara, sarkin na gayyatan dubban Musulmai daga fadin duniya domin su yi Hajji ko Umrah a matsayin bakinsa na musamman.
Ma’aikatar da ke kula da harkokin Musulunci, ce ke kula da shirin.
A Jeddah, manyan jami’an kasar Saudiyya da ma’aikatan filin jirgi sun yiwa tsohon mahajjacin mai shekara 130 tarba na musamman.
KU KARANTA KUMA: Wani bawan Allah ya bai wa Fatima, yarinyar da ke tafitayar kilomita 2 zuwa makaranta kyautar abun hawa (hotuna)
A halin da ake ciki mun ji cewa a yammacin ranar Alhamis ne kotun koli ta kasar Saudiyya ta tabbatar da ganin jaririn watan Dhul Al-Hijjah.
A saboda haka, za a fara aikin Hajji daga ranar Juma'a, 9 ga watan Agusta. Mahajjata zasu hau dutsen Arafat ranar 10 ga watan Agusta, sannan a fara Eidh Al-Adha ranar 11 ga watan Agusta.
Ya zuwa yanzu hukumar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ba ta tabbatar wa da Musulmin Najeriya ranar da za a yi sallah ba, sai dai ana saka ran hukumar zata iya fitar da sanarwa kowanne lokaci daga yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng