Kasar Saudiya ta tsayar 10 ga Agusta a matsayin ranar Arafat, Sallah ranar Lahadi

Kasar Saudiya ta tsayar 10 ga Agusta a matsayin ranar Arafat, Sallah ranar Lahadi

Da yammacin ranar Alhamis ne kotun koli ta kasar Saudiyya ta tabbatar da ganin jaririn watan Dhul Al-Hijjah.

A saboda haka, za a fara aikin Hajji daga ranar Juma'a, 9 ga watan Agusta. Mahajjata zasu hau dutsen Arafat ranar 10 ga watan Agusta, sannan a fara Eidh Al-Adha ranar 11 ga watan Agusta.

Ya zuwa yanzu hukumar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ba ta tabbatar wa da Musulmin Najeriya ranar da za a yi sallah ba, sai dai ana saka ran hukumar zata iya fitar da sanarwa kowanne lokaci daga yanzu.

Ba kasafai Musulman Najeriya ke saba ranar Sallah da kasar Saudiyya ba, suna yin Sallah ne rana daya.

Kimanin maniyyata 1,249,951 ne suka sauka a ksar Saudiyya domin aikin hajjin bana, kamar yadda sashen kididdiga na ofishin bayar da fasfo din kasar Saudiyya ya sanar ranar Laraba.

Maniyyata daga kasashen Pakistan, Bangladesh, Indonesia, Malaysia da Tunisia, na ciga da sauka a kasar domin gudanar da aikin hajji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel