Kungiyar ISWAP ta kashe sojoji 25 a Borno

Kungiyar ISWAP ta kashe sojoji 25 a Borno

Aukuwar mummanan hari na wani reshen mafi munin kungiyar ta'adda a duniya IS cikin jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Najeriya, ya salwantar da rayukan dakarun sojoji 25 kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Rahotanni dake zuwa mana a yanzu sun tabbatar da cewa, wani mummunan hari da wani reshen mafi munin kungiyar ta'adda a duniya wato IS da ya auku a yankin Arewa maso Gabas, ya salwantar da rayukan dakarun sojin Najeriya 20 da kuma na kasar Chadi biyar.

Wata majiyar rahoto ta dakarun soji, ta tabbatar da wannan mummunan rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan 2019.

Mayakan kungiyar ISWAP (Islamic State West African Province) da ke yankin Yammacin Afirka, wani reshe na kungiyar ISIS mai daula a kasar Syria da Iraqi, ita ce ke da alhakin wannan mummunan hari da ya auku a gabar tafkin Chadi.

Mummunan harin mayakan ISWAP da ya auku da sanyin safiyar ranar Litinin cikin garin Baga da ke iyaka da gabar tafkin Chadi, ya salwantar da rayukan dakarun sojin Najeriya 20 yayin da kuma na kasar Chadi 5 suka riga mu gidan gaskiya.

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta ruwaito a ranar 22 ga watan Agustan 2014, Amurka ta ce kungiyar IS da ke kiran kanta Daular musulunci, ita ce barazana mafi hadari da ta taba fuskanta a lokacin nan, kuma ta ce wajibi ne ta murkushe ta.

KARANTA KUMA: Dogaro da kai da sauran dalilai 4 da ya kamata mutum ya koyi sana'ar hannu

Hakazalika, a yayin da a makon nan ne kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta cika shekaru goma da daura damarar ta'addanci a Najeriya, majalisar dinkin Duniya ta ce akalla mutum 27,000 ne suke rasa rayukansu a tsawon shekara goma na rikicin kungiyar a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel