Direban mota da ya maidawa wani mutumi $2400 da ya manta da su a Legas

Direban mota da ya maidawa wani mutumi $2400 da ya manta da su a Legas

Wani Bawan Allah mai suna Olayinka Adeniyi wanda ya ke sana’ar kabu-kabu na hayar mota a babban filin jirgin Najeriya da ke Legas, ya tsinci kudi masu yawa, kuma ya maidawa mai shi.

Kamar yadda mu ka samu labari Mista Olayinka Adeniyi ya tsinci kudi ne da wani Fasinjansa ya manta da su a cikin ambula a motarsa. Wannan kudi $2400 sun kai N880, 000 a kimar Najeriya.

Wannan Mutumin Allah ya ajiye mai kudin abinsa a tashar jirgin. Wannan abu ya faru ne a Ranar Laraba da dare a cikin Garin Legas bayan ya dauki fasinjar daga filin jirgi na Murtala Muhammed.

Adeniyi ya ce bai saba daukar abin da ba na shi ba domin kuwa idan ya yi haka, zai jefa wasu Bayin Allah a cikin wahala. Adeniyi ya lura da kudin ne bayan ya sauke fasinjan a Unguwar Ibese.

“Mun yi ciniki da shi, na yarda zan kai shi Ibese a Ikorodu a kan N6, 000.”

“Na yi maza na kamo hanya na dawo filin jirgi bayan na ajiye sa a gidansa.”

“Ajiye mota ta ke da wuya bayan na dawo, sai na hangi wata ambula a kujerun baya.”

KU KARANTA: Wani Soja mai suna Bashir Umar Soja ya tsinci $415000 ya yi cigiya

“Ko da na dauka sai na bude.”

“Abin da gani su ne takardun fasfonsa. Da na kura idanu da kyau, sai na lura akwai wata farar ambula a cikin takardar.”

“Ina lalubawa sai na tsinci kudi a ciki ‘Yan Dalar Amurka $100 har guda 24.”

A nan ne Adeniyi ya ajiye wannan ambula a cikin ofishin kungiyarsu ta Direbobin filin jirgin watau ACHAN. Dele Ayeni wanda ya manta da wannan kudi ya bayyana abin da ya wakana.

Wannan abu ya faru ne da kimanin karfe 1:30 na dare bayan Mista Dele Ayeni ya dawo daga Kasar Masar inda ya yi kuskuren jefar da ambularsa a cikin mota kuma bai lura ba har sai kashegari.

Ayeni ya ce Maidakinsa ta ba shi shawarar ya zo filin jirgin ya yi cigiya, kuma a ka yi sa’a ya dace. Wannan Mutumi ya yabawa gaskiyar Direbobin. ACHAN ta ce ta saba ganin irin wannan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel