An kira mutum 80, 724 domin yin gwajin karshe na shiga aikin ‘Dan Sanda
Mutane 80,724 ne sunayensu ya samu fitowa cikin wadanda za a dauka aikin ‘yan sanda a Najeriya. Daga ciki dai za a dauki mutum 10, 000 ne rak wannan aiki kamar yadda hukumar NPF ta bayyana.
Hukumar ‘yan sandan Najeriya za ta dauki mutane 10,000 ne a matsayin sababbin kuratan ‘yan sanda. Za a yi gwajin daukar aikin ne a karshen makon nan a ranar 3 ga Watan nan Agustan 2019.
‘Yan sandan kasar sun bayyana wannan ne ta bakin babban jami’in yada labarai da hulda da jama’a, Ikechukwu Ani. Ani ya fitar da wannan jawabi ne a Ranar Talata, 30 ga Watan Yuni, 2019.
Za a yi wannan gwaji ne a fadin jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Wannan ya na cikin manufar shugaba Muhammadu Buhari na bunkasa sha’anin tsaron kasar.
KU KARANTA: Za a baza na’urori CCTV a kan tituna saboda inganta tsaro a Najeriya
Kafin yanzu gwamnatin Buhari ta dauki wasu dubunnan a matsayin sababbin jami’an ‘yan sanda. Wannan zai sa a kama hanyar cike gurbin da a ke da su na karancin jami’an tsaro a Najeriya.
An samu fiye da mutane 315, 000 da ke neman shiga wannan aiki na ‘dan sanda. Da farko an zabi mutane 210, 150, daga baya a ka rage yawansu zuwa mutum 80, 724 da su ka kai matakin karshe.
Kakakin ‘yan sandan Najeriya ya bayyana cewa yanzu haka a na ta faman aikawa wadanda za su yi wannan jarrabawa ta karshe sakonni ta lambar wayoyinsu domin sanar da su game da shirin.
Za a fara wannan gwaji ne a Ranar Asabar mai zuwa da kimanin karfe 8:00 na safe. Hukumar za ta fitar da sunayen wadanda a ka zaba a manyan ofisisoshinta da ke ko ina a fadin Najeriya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng