An gano wuri da aka birne sojoji fiye da 1000 da Boko Haram suka kashe - Rahoto

An gano wuri da aka birne sojoji fiye da 1000 da Boko Haram suka kashe - Rahoto

Wani rahoto da jaridar Amurka ta Wall Street Journal ta wallafa ya ce an birne fiye da sojojin Najeriya 1,000 a wani boyeyen makabarta da ke garin Maimalari a jihar Borno ba tare da yi musu karramawa irin ta sojoji ba.

Rahoton ya ce, "An yi amfani da fitilar tocila ne aka birne wannan sojojin a cikin ramuka da wasu sojoji ko mazauna kauyen suka gina kuma aka biya su daloli kalilan."

Kazalika, a kan kwaso gawarwarkin wasu sojojin daga dakin ajiyar gawa na asibitoci cikin dare a manyan motocci a birne su idan wuraren ajiye gawarwakin sun fara karanci a asibiti a cewa wasu sojojin da suke nemi a boye sunansu da manyan jami'an gwamnati da wakilan Najeriya a kasashen waje.

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe ya budurwarsa bayan ta raina kwazonsa a gado

"An birne wasu daga cikin abokai na a kaburburan da ba zan iya ganewa ba a cikin dare," a cewa wani soja a barikin sojoji na Maimalari inda sama da sojoji 1000 ke zaune.

"Suna mutuwa kuma katse su daga cikin tarihi."

Boyeyen makabartan na Maimalari ba shine kadai irinsa da ake da shi a yankin Arewa ta Gabas ba a cewa wani babban jami'in gwamnati.

"... Akwai a kalla kaburburan sojoji 1,000 a makabartan ta sirri a Maiduguri da kuma sananiyar makabartan da ke sansanin sojoji na sojojin Najeriya da ke Maiduguri na sojojin da Boko Haram suka kashe a cewar wasu sojoji da wasu jami'an soji, wasu ma sun ce adadin ya fi haka," inji rahoton.

"An killace wasu gonaki saboda a samu wurin da za a rike birne sojoji," a cewar Sarah James, wata manomiya mai shekaru 50 matar wani soja da ya yi murabus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel