Gwamna Yahaya ya mayar da makarantar almjirai ta horon Malaman makarantun Boko
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya, ya bayar da umarnin mayar da makarantar almajirai, da gwamnatin PDP ta gina, ta horon malaman makaranta.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne a ranar Talata yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai makarantar, wacce aka gina a kan miliyan N360, a karamar hukumar Kwami.
Ya ce mayar da makarantar kwalejin horon malamai zai taimaka wa yunkurin gwamnati na inganta harkar ilimi.
"Na zo na ga yadda wurin ke neman lalacewa saboda rashin kulawa da kuma yin amfani da shi tun bayan kaddamar da shi a shekarar 2015.
" Kamar yadda ku ka gani, komai na wurin a lalace yake, iska da ruwan damima sun lalata rufin wurin gaba daya," a cewar gwamnan.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa zata yi hakan ne domin ganin cewa ba a yi asarar dukkan kudin da aka kashe wajen gina makarantar ba.
"Maimakon kawai a bar ginin ya cigaba da lalacewa, shine muka ga cewa gara mu yi amfani da wurin domin yin wani abu da kowanne dan jihar Gombe zai ci moriyarsa, ba iya kawai ma karamar hukumar da aka yi ginin ba," a cewar gwamnan.
DUBA WANNAN: Wata matar aure ta nemo wa mijinta mata ta biyu yayin da ta dauki juna biyu
Sannan ya cigaba da cewa, "ina fatan yin hakan zai taimaka wajen bawa gwamnati damar inganta ilimi a matakin farko ta hanyar bawa malamalaman makarantu horo a kan hanyoyin da zasu bawa yara ilimi mai nagarta da inganci."
Ya ce gwamnatinsa zata inganta wurin domin yin daidai da tsarin wurin bayar da ilimi da kuma morewar malaman da zasu karbi horo a wurin.
Dakta Abubakar Kumo, sakatare a hukumar ilimi ta jihar (SUBEB), ya shaida wa gwamnan cewa ba a taba amfani da wurin ba tun da aka gina shi a shekarar 2015.
Ya ce an yi ginin ne da niyyar tsarin karatun almajirai a karkashin hukumar ilimin bai daya ta kasa (UBEC).
Ya kara da cewa, ginin na dauke da ajin karatu guda 10, dakin kwanan dalibai da malamai, dakin cin abinci da sauransu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng