China za ta fara yi wa Najeriya gwanjon motocin hawa – Minista

China za ta fara yi wa Najeriya gwanjon motocin hawa – Minista

Kasar Sin watau China za ta soma fita da motoci waje zuwa Nahiyoyin Afrika da Turai da kuma cikin kasashen Yankinta na Asiya. Najeriya na cikin inda China za ta fara shigo yi wa gwanjon motoci.

Kamar yadda mu ka samu labari daga ma’aikatar kasuwanci na kasar ta Sin, za a shigo da wasu daga cikin motocin da a ka yi amfani da su zuwa Najeriya domin a saidawa jama’a a matsayin gwanjo.

A halin yanzu Kasar Sin ta samu damar aika wadannan motoci zuwa wasu manyan Garuruwa 10, daga ciki har da Najeriya, inda za a saida gwanjon motoci 300 ne da nufin bunkasa tattalin kasar wajen.

Ma’aikatar kasuwancin Kasar Sin ta kirkiro wannan shiri ne domin babbako da sha’anin saida motoci da ya ke nema ya yi kasa a karon farko tun shekarar 2019. Jaridun waje su ka rahoto mana wannan.

KU KARANTA: Wani kamfanin kasar waje zai fara kera motoci a Najeriya

Kafin yanzu, kasar ta Sin ba ta fita da motocin da ta kera zuwa ketare. Sai dai ganin tattalin arzikin ta ya fara karyewa a bara ya sa kasar ta fara canza tunani inda ta ce za ta rika fita kasashen waje.

A 2017, kasashen da ke kera motoci a Duniya sun fitar da motoci kusan miliyan 40 zuwa ketare. A na sa rai cewa a yanzu yawan motocin da a ke kai wa kasashen Duniya za su kara yawa a halin yanzu.

A Najeriya, akalla 80% na motocin da ake hawa, an taba amfani da su a waje. Wannan ya sa China ta ga cewa zai yi kyau ta yi kasuwanci da Najeriya wajen saida gwanjon motocin da jama’a za su hau a saukake.

Ma’aikatar kasuwancin na Sin ta na ganin cewa za a samu alheri kwarai idan kasar ta shiga kasuwar saida motoci a kasar waje. A Najeriya, a na kuka da harajin da a ka daura wajen shigowa da motoci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel