An kuma: An kai wa fitaccen dan wasan Barcelona Lionel Messi hari a wani gidan rawa

An kuma: An kai wa fitaccen dan wasan Barcelona Lionel Messi hari a wani gidan rawa

- A daren ranar Lahadin nan ne da ta gabata, 28 ga watan Yulin shekarar 2019, aka kai wa dan wasan Barcelona Lionel Messi hari

- An kai wa dan wasan harin ne a lokacin da yaje garin Ibiza shi da matarsa da 'ya'yansu guda uku domin yawon shakatawa

- Harin dai an kai wa dan wasanne a wani gidan rawa, inda har ya zuwa yanzu an kasa gano mutumin da ya kai wa dan wasan harin

An samu wani dan hargitsi a wani gidan rawa dake Ibiza a lokacin da tauraron kungiyar Barcelona da kuma kasar Argentina, Lionel Messi aka bada rahoton cewa wani mutumi da har yanzu ba a gano ko waye ba ya kai masa hari a lokacin da ake kan cashewa a gidan rawar.

Lamarin ya faru da cikin daren ranar Lahadi ranar 28 ga watan Yuli, shekarar 2019.

Dan wasan kwallon kafar yana yawon shakatawa ne da matarsa Antonela Roccuzzo mai shekaru 31, da kuma 'ya'yansu guda uku; Thiago mai shekara 6, Mateo mai shekara 3 da kuma Ciro mai shekara 1, bayan su kuma akwai wasu abokanansa, wanda suka je garin na Ibiza tare.

KU KARANTA: To fah: Tunda nake ban taba yin waka na ciwa wani mutunci ba - Rarara

A cikin bidiyon da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta, ya bayyana yadda jami'an tsaro suka samu suka fita da dan wasan daga gidan rawar bayan mutane sun mamaye wajen suna kallon lamarin dake faruwa.

Har yanzu ba a tabbatar da abinda ya jawo wannan hari da aka kai wa dan wasan ba, sai dai akwai wasu mutane da ke tambaya ko dan wasan yayi wani abu ne da yasa aka kai masa harin a gidan rawar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel