Zakzaky: Sultan da shugabannin addinin musulunci su shiga tsakanin gwamnati da 'yan shi'a - Shehu Sani

Zakzaky: Sultan da shugabannin addinin musulunci su shiga tsakanin gwamnati da 'yan shi'a - Shehu Sani

  • Sanata Shehu Sani ya shiga cikin takaddamar rikicin da ke tsakanin mabiya akidar shi'a da kuma gwamnatin tarayya.
  • Sanatan ya wassafa wasu shawarwari hudu da yake ganin zasu magance takaddamar a kasar nan
  • Tsohon wakilin jihar Kaduna a zauren majalisar dattawa ya nemi Sarkin Musulmi yayi amfanin da rawanin sa wajen shiga cikin lamarin

A ranar Lahadi 28 ga watan Yuli, Sanata Shehu Sani, ya shimfida wasu shawarwari hudu da yake ganin zasu kawo karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa dake tsakanin gwamnatin Tarayya da kuma kungiyar IMN da aka fi sani da kungiyar shi'a.

Shawarwarin Sanatan na zuwa ne a yayin da ya kai ziyara jihar Kano inda ya ce ayyana kungiyar shi'a a matsayin 'yar ta'adda bisa zarginta da haifar da husuma ta salwantar rayuka da asarar duki ba zai magance matsalar ba illa iyaka kara ta'azzara da lamarin zai yi.

A ranar Juma'a babbar kotun tarayya dake garin Abuja, ta zartar da hukuncin haramta kungiyar IMN ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky, jagoran 'yan shi'a na Najeriya. Bayanan kotun sun nuna cewa hukuncin ya yi daidai da bukatar gwamnatin tarayya.

Sanata Shehu Sani wanda ya kasance tsohon wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa, ya ce wannan hukunci da kotun ta zartar na cin karo da tabbatuwar zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma ingancin tsaro a kasar nan.

A baya-bayan nan, tashin hankali ya kazanta a tsakanin jami'an tsaro na 'yan sanda da magoya bayan kungiyar IMN, wadanda ke ci gaba da zanga-zanga akai-akai tun bayan tsare shugaban su da gwamnati tayi a shekarar 2015.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sanata Shehu Sani bisa ga ra'ayi yayi shimfidar wasu shawarwari hudu da zau kawo karshen wannan tashin-tashin dake tsakanin gwamnati Najeriya da kuma maboya bayan akidar shi'a a kasar.

Tsohon Sanatan ya nemi sarkin musulmi Sa'ad Abubakar da sauran mashahuran malaman addinin musulunci da su tsaya a matsayin lamuni domin sakin Sheikh Zakzaky tare da mai dakin sa Zeenatu dake tsare a hannun gwamnatin tun tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Shawara ta biyu da Sanatan ya shimfida ita ce neman magoyan bayan akidar shi'a da su dakatar tare da daina duk wata zanga-zanga walau ta lumana ko sabanin haka.

KARANTA KUMA: Ciwon ciki da sauran alamomi 5 na cutar hanta

Ta ukun shi ne gwamnati ta nemi hanyar warware matsalolin da suka yi sanadiyar salwantar rayuka da kuma asarar dukiya ta mabiya akidar shi'a kamar yadda kotu ta bayar da umarni a baya.

Shawara ta hudu kamar yadda Sanata Shehu Sani ya zayyana, ita ce kiran kungiyar IMN da ta raba gari da duk wata kungiya a kasashen ketare masu yiwa al'amuran kasar nan katsalandan. Ya ce hakan na barazana ga harkokin tsaro na kasa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel