Aisha Buhari ta yi kira ga jama’a da su kokarin kallon fim din Hausa mai suna Hauwa Kulu

Aisha Buhari ta yi kira ga jama’a da su kokarin kallon fim din Hausa mai suna Hauwa Kulu

Uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta yi kira ga jama’a da su yi kokari su kalli wani shararren fim din Hausa na Kannywood mai suna Hauwa Kulu.

Uwargidar Shugaban kasar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa kada wanda ya bari aka barshi a baya wajen kallon wannan ingantaccen fim din na kamfanin Maishadda.

Wannan nan dai shine karo na farko da Aisha Buhari ke tallata wani abu da ya shafi fim.

KU KARANTA KUMA: Mansurah Isah ta nemi Hadiza Gabon da Maryam Yahaya su yi karan Tanimu Akawu kan kalaman cewa matan Fim suna bin mazan banza

Ga yadda ta wallafa a shafin nata:

A wani labari na daban, mun ji yadda shahararren jarumin wasan Hausan nan na masana'antar Kannywood, Alhaji Tanimu Akawu, wanda ya bayyana cewa yanzu haka ya kai kimanin shekaru goma sha takwas yana fafatawa a harkar fim.

A wata tattaunawa da aka yi dashi a wani gidan rediyo mai suna Human Right dake garin Abuja, cikin shirin dandalin fina-finai, jarumin ya bayyana cewa matan fim din suna bin mazan banza masu kudi da masu mulki.

Jarumin ya bayyana cewa motar da Hadiza Gabon ke hawa kadai za ta iya siyan motocinsa guda goma, ya kara da cewa shi EOD ce yake hawa kuma ya siye ta da kudin shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel