'Yan wasa: Messi, Ronaldo, da Neymar sun yi zarra a Duniya wajen samun kudi

'Yan wasa: Messi, Ronaldo, da Neymar sun yi zarra a Duniya wajen samun kudi

Mujallar Forbes ta fitar da jerin ‘yan wasan da su ka fi kowa samun albashi a wannan shekara ta 2019. Jerin na dauke da manyan ‘yan wasan kwallon kafa da Mawakan da su ka yi fice a Duniya.

Rahoton na Forbes ya nuna cewa Lionel Messi ne wanda ya fi kowa albashi a cikin ‘yan wasan kwallon. A cikin watanni 12 da su ka wuce, ‘Dan wasa Messi ya tashi da fam miliyan £101.

Kamar yadda Forbes ta bayyana, Messi ya na bayan Taylor Swift, Kylie Jenner da Kanye West a cikin jerin masu kudin ‘yan wasan. Kowanen su ya samu fiye da fam miliyan £120 a shekarar nan.

‘Dan wasan na kungiyar Barcelona ya na samun fam miliyan £9.5 daga kwangilar da ya shiga da kamfanin Adidas. Wannan kuma bayan albashinsa duk shekara a kungiyar na fam miliyan £64.

A cikin ‘yan wasan kwallo, 'dan wasa mai shekaru 34, Cristiano Ronaldo ne na biyu. A cikin shekara daya, tsohon ‘dan kwallon na kungiyar Real Madrid ya samu kusan fam miliyan £86.5.

KU KARANTA: Super Eagles ta yi sama a jadawalin kasashe na kwallon kafa

A yanzu Ronaldo ya na karbar fam miliyan £51 a Juventus. A ranar farko da ya je kungiyar, sai da a ka saida rigunansa fiye da 520, 000. Ronaldo ne na shida idan a ka hada da sauran ‘yan wasa

Na uku a jerin ‘yan kwallon, kuma na bakwai a Duniya shi ne Neymar Jr. ‘Dan wasan na Brazil ya tashi da fam miliyan £83.5 a daidai wannan lokaci. Neymar ya na taka leda ne a kasar Faransa.

A cikin sauran ‘yan kwallon kafa na Duniya, babu wanda sunansa ya iya shiga cikin mutane 100 da Forbes ta bayyana na wadanda su ka samu makudan kudi a cikin wannan shekarar ta 2019.

Ga cikakken jerin nan mai dauke da sunayen Attajiran ‘yan wasan kwallon kafa da sauran ‘yan wasa masu buga kwallon kwando da ‘yan wasan tanis a bana. Jerin na dauke da mutum 10.

1. Lionel Messi (£101m)

2. Cristiano Ronaldo (£86.5m)

3. Neymar (£83.5m)

4. Canelo Alvarez (£75m)

5. Roger Federer (£74.5m)

6. Russell Wilson (£71.4m)

7. Aaron Rogers (£71.2m)

8. LeBron James (£71m)

9. Steph Curry (£63.7m)

10. Kevin Durant (£52.1m)

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng