'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindigan Katsina, sun kwato shanu da tumaki 500

'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindigan Katsina, sun kwato shanu da tumaki 500

Jami'an tawagar Operation Puff Adder a Katsina a ranar Juma'a sun dakile wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai a garuruwan Sabon Garin Baure da kauyen Baure da ke karamar hukumar Safana na Jihar.

An ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan bindigan sun samu raunin bindiga kafin suke tsere zuwa kan iyakar dajin Rugu da ke karamar hukumar.

Mai magana da yawun Rundunar 'Yan sandan Katsina, Gambo Isah ya tabbatar da labarin.

Ya ce har yanzu ba a kama 'yan bindigan ba amma jami'an tsaro sun bazama nemansu a cikin garuruwan biyu.

Isah ya ce 'yan bindiga 200 ne suka kai farmaki garuruwan biyu a safiyar ranar Juma'a kafin jami'an tsaron su fattatake su.

DUBA WANNAN: An kama tsohon dan majalisa bisa zargin safarar bindigu da garkuwa da mutane

Ya ce, "A ranar 26 ga watan Yuli misalin 12.00 na dare wata tawagar 'yan bindiga kimanin su 200 dauke da muggan makamai suna harbe-harbe sun kai farmaki kan mazauna kauyukan Sabon Garin Baure da Baure da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina.

"Nan take, DPO na garin Safana ya jagoranci tawagar Operation Puff Adder zuwa garuruwan domin tunkarar 'yan bindigan inda su kayi musayar bindiga na tsawon sa'a daya. 'Yan sandan sunyi nasarar fatattakar 'yan bindigan daga kauyen.

"Sun kuma kwato shanu 200 da akuyoyi da raguna 300 da babura 300 daga hannun 'yan bindigan. A halin yanzu 'Yan sandan na bin sahun 'yan bindigan da suka tsere da raunin bindiga domin kama su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel