An tsinci gawar soja da wani rubutu a takarda a barikin sojoji a Abuja

An tsinci gawar soja da wani rubutu a takarda a barikin sojoji a Abuja

Labarin da Legit.ng ke samu yanzu yanzun nan daga kafar yada labarai ta TVC na nuni da cewa an tsinci gawar wani soja a barikin sojojin Mambila da ke birnin tarayya, Abuja.

Sojan, da mahukunta suka boye sunansa, ya bar wani rubutu a jikin takarda a wurin da saka samu gawarsa.

Har yanzu hukumar rundunar soji ba ta fitar da wani jawabi ba a hukumance dangane da samun gawar sojan, amma wata majiya ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike.

Ana zargin cewa jami'in sojan ya kashe kansa ne.

Za mu kawo karin bayani da zarar rundunar soji ta fitar da jawabi dangane da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng