Shugaba Buhari zai daga zuwa kasar Liberia don halartar taro da kuma karbar wata muhimmiyar kyauta a kasar

Shugaba Buhari zai daga zuwa kasar Liberia don halartar taro da kuma karbar wata muhimmiyar kyauta a kasar

- Shugaban kasa Buhari zai daga zuwa kasar Liberia a ranar Juma'a, 26 ga watan Yuli

- Buhari zai halarci taron bikin samun 'yancin kan kasar sannan zai karbi lambar yabo na musamman a kasar

- Daga cikin wadanda za su masa rakiya akwai gwamnoni uku, sakataren dindindin na ma'aikatar harkokin waje da wasu manyan jami'an gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Juma’a, 26 ga watan Yuli zuwa Monrovia, kasar Liberia domin halartan bikin zagayowar raanar yancin kan kasar karo na 172.

Bayan kasancewarsa babban bako na musamman a wajen taron, za a karrama Shugaban kasar da karramawa mafi daraja a kasar.

A wani jawabi daga babban hadimin Shugaban kasar a kafofin watsa labarai, Garba Shehu, ya kuma bayyana cewa gwamnatin kasar ce za ta gabatar da lambar yabon ga Buhari akan kokarinsa kan lamuran kasashen duniya, gwamnati, addini, da dai sauransu.

Shugaban kasar zai samu rakiyar wasu gwamnoni da suka hada da Kayode ayemi, Abdulrahman Abdulrazaq da kuma Mai Mala Buni.

Sauran masu rakiyan sun hada da sakataren dindindi na ma’aikatar harkokin waje, Ambasada Mustapha Sulaiman da sauaran manyan jami’an gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Anyi musayar yawu tsakanin Atiku da Buhari kan takunkumin hana shiga Amurka

Ana sanya ran Shugaban kasar zai dawo gida ajeriya a wannan rana ta Juma’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel