Jerin Ministoci: APC reshen Enugu ta nuna rashin amincewa da sake zabar Onyeama

Jerin Ministoci: APC reshen Enugu ta nuna rashin amincewa da sake zabar Onyeama

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Enugu ta nuna rashin amincewa da sake zabar tsohon ministan harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, ta bayyana lamarin a matsayin “mummunan kuskure.”

Tace duba ga rashin kokarin da Onyeama yayi a lokacin mulkin Shugaban kasar na farko, irin wannan “bai cancanci yin komai ba a ajandar Next Level na mulkin APC."

Da yake martani akan sake nadin Onyeama, wanda sunansa ya kansance daga cikin zababbun ministoci 43 da shugaba kasar ya aika majalisar dattawa domin tabbatar dasu, Shugaban jam’iyyar APC a Enugu, Dr. Ben Nwoye yace lamarin ya saba ma ra’ayin jihar Enugu da ma yan Najeriya baki daya.

Ya bayyana cewa tsohon ministan harkokin wajen bai tabuka wani abun kirki bag a jam’iyyar APC reshen Enugu a lokacin da yake a matsayin minista.

A cewar Nwoye, maimakon ya hada hannu da shugabannin APC a jihar wajen tabbatar da ci gaban jam’iyyar, Onyeama “ya mayar da hankali wajen almubazaranci da kudin masu biyan haraji wajen daukar nauyin rikice-rikice."

KU KARANTA KUMA: Manyan yan Najeriya sun jinjina wa shugaba Buhari akan zabinsa na ministoci

Shugaban ya dage cewa sake nada tsoho ministan zuwa majalisar tarayya zai ci gaba da lalata jam’iyyar a jihar Enugu, saboda “wannan mutum ne wanda yayi kaurin suna wajen dabanci da lalata tsarin jam’iyyar.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel