Sojoji sun kashe 'yan bindiga 78, sun kwato bindigu masu yawa a Zamfara

Sojoji sun kashe 'yan bindiga 78, sun kwato bindigu masu yawa a Zamfara

Dakarun Sojojin Najeriya ta ce dakarunta na 'Operation Hadarin Daji' sun kashe 'yan bindiga 78 a wurare daban-daban a dazukan jihar Zamfara cikin watanni biyu da suka gabata.

Sojojin sun yi nasarar ceto mutane 50 da 'yan bindigan ke garkuwa da su yayin da suka kwato bindigu kirar AK 47 guda shida da machine gun guda daya da bindigar farauta 14 da kananan bindigu 3 da alburussai 2,437.

Mukadashin mai magana da yawun sojin, Kwanel Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

DUBA WANNAN: Sabo Nanono: Abinda ya kamata ku sani game da zababen Ministan Buhari daga Jihar Kano

Ya yi bayanin cewa a halin yanzu an fara gudanar da bincike kan wadanda aka kama inda ya ce za a mika su ga hukumomin tsaro domin a gurfanar da su gaban hukuma.

Nwachukwu ya ce, "An kaddamar da Operation Hadarin Daji ne domin magance kallubalen tsaro da ake fuskanta a wasu jihohin Arewa.

"A cikin watanni biyu da fara atisayen hadin gwiwar, dakarun sojojin sun yi aragama da 'yan bindigan inda suka ceto wadanda aka yi garkuwa da su 50 kuma suka kashe 'yan bindiga 78 a wurare daban-daban a jihar Zamfara.

"An kuma kama sama da mutane 25 da ake zargin mahara ne tare da kwato babura 14 a hannunsu. A halin yanzu ana gudanar da bincike kan wadanda aka kama sannan daga bisani za a mika su ga hukumomin tsaro da za su gabatar da su a kotu."

A yayin da ya ke tsokaci kan Operation Thunder Strike da aka kaddamar domin yaki da masu garkuwa da mutane a kan titin Kaduna zuwa Abuja, Kakakin Sojin ya ce sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane shida tare da kama wasu 14 cikin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel