Tsaffin Sanatoci da suka samu nadin minista a sabuwar gwamnatin Buhari

Tsaffin Sanatoci da suka samu nadin minista a sabuwar gwamnatin Buhari

Tsaffin gwamnoni bakwai da kuma sanatoci na cikin jerin ministoci 43 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunayensu a ranar Talata zuwa majalisar dattawa domin tantancewa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, tsaffin sanatocin bakwai da suka samu shiga cikin sabuwar majalisar zantarwa a wa'adin gwamnatin Buhari na biyu sun hadar da:

Sanata Gbemisola Saraki (Kwara), Sanata Olorunnibe Mamora (Legas), Sanata Hadi Sirika (Katsina), Sanata Tayo Alasoadura (Ondo), Santa Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Sanata Chris Ngige (Anambra) da kuma Sanata George Akume (Benuwai).

Tsaffin gwamnonin da suka shiga sun hadar :

Rauf Aregbesola (Osun), George Akume (Benuwai), Niyi Adebayo (Ekiti), Rotimi Amaechi (Rivers), Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Timipre Sypva (Bayelsa), da kuma Babatunde Fashola (Legas).

Bayan shafe tsawon fiye da kwanaki 50 da karbar rantsuwa ta sabuwar gwamnatin sa a wa'adi na biyu wanda aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, shugaban kasa Buhari ya fidda jerin sunayen sabbin ministocin sa tare da neman amincewar majalisar tarayya.

KARANTA KUMA: Sabbin Ministocin Buhari daga jihohin Arewa

A gobe Laraba 24 ga watan Yuli, majalisar za ta fara tantance sabbin minstocin kamar yadda Sanata Ahmed Lawan ya bayyana. Za a fara tantacewar daga jihar Abia kuma a kare da jihar Zamfara.

Hakazalika akwai kuma Honarabul Emeka Nwajiuba, tsohon dan majalisar wakilai na jihar Imo a jam'iyyar AP (Accord Party) da ya samu shiga cikin nadin ministocin da Buhari yayi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel