Ba mu goyon bayan Bello ya zarce a mulki – Inji wata Kungiyar Igala

Ba mu goyon bayan Bello ya zarce a mulki – Inji wata Kungiyar Igala

Wasu daga cikin Kabilar Igala da ke karkashin lemar kungiyar Ukomu Igala, sun nuna cewa ba su tare da mubaya’ar da Mai martaba Attah na Igala ya yi wa gwamna mai-ci watau Yahaya Bello.

Yayin da a ke shirin zabe, wadannan mutane na Kabilar Igala da ke zama a Kaduna sun nuna cewa ba za su taba mara baya ga gwamnan da ya shafe watanni 28 ba tare da ya biya albashi ba.

Wannan kungiya ta ‘Yan Igala Mazauna Kaduna sun fito karara su na bayyana adawarsu ga gwamna Yahaya Bello wanda ya ke neman tazarce a zaben bana a karkashin jam’iyyar sa ta APC.

Wani Dattijo mai suna Injiniya Samuel Salifu ne ya yi wannan jawabi a madadin daukacin kungiyar Ukomu Igala da ke Garin Kaduna. Salifu ya ce gwamnatin Bello ta jefa mutane a kangi.

KU KARANTA: Rikicin cikin-gidan da ya barkowa APC a Edo ya ki cinyewa

Injiniya Salifu ya bayyana cewa za su bada goyon bayansu ne ga ‘dan takarar gwamnan da ke da burin jama’an jihar Kogi a zuciya, ba wanda bai yi wa al’umma aikin komai da za a zo a gani ba.

Mai magana da bakin kungiyar ya ce: “Mu Ukomu Igala, ba mu tare da wannan mubaya’a da Sarakuna su ka tattara su ka bi gwamna zuwa gaban shugaban kasa domin nuna su na tare da shi.”

Ya kara da cewa: “Yaushe mutanen Igala za su goyi bayan wanda ya ke sukar matan Igala, ko gwamnan da ya ke cika-bakin cewa babu mutumin Igala da ya isa ya tsaya takara tare da shi?”

Wannan Dattijo ya sake karawa da cewa ba za su zabi gwamnan da ba zai iya gyara hanyoyin babban Birni na Garin Lokoja ba, inda su ka ce, ko da za ayi amfani da ‘yan daba, ba za su zabi Bello ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel