Yadda aka kashe min miji a harin kyamar bakar fata a kasar Kyrgyzstan - Amina Aliyu

Yadda aka kashe min miji a harin kyamar bakar fata a kasar Kyrgyzstan - Amina Aliyu

An kashe Aliyu Tijjani Abubakar, wani matashi mai shekaru 38, dan asalin jihar Kaduna, a Bishkek, babban birnin kasar Kyrgyzstan, a wani harin nuna kyamar bakar fata. Marigayin da ke aiki a kasar bayan kammala karatunsa, na zaune ne tare da iyalinsa a Bishkek.

Ya kammala karatunsa a jami'ar Alatoo ta kasa da kasa, wacce ke da alaka da jami'ar Nile Turkish da ke Abuja. Ya cigaba da zama a Bishkek inda ya kafa wata makarantar koyar da Turanci mai suna 'Cambridge English School' domin koyar da harshen Turanci ga duk daliban da ke da son iya yaren a matsayin yare na biyu.

A ranar 5 ga watan Yuli ne aka samu rahoton mutuwar Abubakar, wanda aka kashe a tsakiyar birnin Bishkek (Bishkek city center).

"Mijina mutum ne mai kirki da kula da iyali sosai," wadannan su ne kalaman matarsa, Amina Aliyu, wacce ta fashe da kuka yayin bayanin yadda aka kashe mata miji. Sun yi murnar cika shekaru biyu da aure a watan Fabrairu, tare da diyarsu mai shekara daya da 'yan watanni.

A cewar kanin Abubakar, Abdurrahman, wanda yanzu haka shi ma dalibi ne a jami'ar Alatoo, wani dan asalin kasar Kyrgyzstan ne ya far wa dan uwansa haka siddan. Ya kara da cewa mutumin ya fara bin Abubakar ne tare da daukan hotonsa yana nuna shi tare da fadin kalamai na nuna kyama. Da farko Abubakar ya yi burus da shi, tare da tsallaka titi domin nesanta kansa daga mutumin, amma sai mutumin ya cigaba da binsa. Bayan Abubakar ya yi wa mutumin magana ne sai kawai ya buge shi a ka, lamarin da ya sa shi faduwa sumamme.

DUBA WANNAN: An gano kasar da ya fito: Mutumin da ya dare jirgin sama ya hana shi tashi a Legas ba dan Najeriya ba ne - FAAN

A faifan bidiyon kisan Abubakar, wanda ya yadu a dandalin sada zumunta, an ga wasu 'yan asalin kasar na zuba masa ruwa, bayan ya suma, ko hakan zai sa ya farfado, amma a banza. An dauke shi zuwa asibiti a Bishkek inda ya mutu bayan kwana biyu.

Yaduwar faifan bidiyon harin da aka kai wa Abubakar keda wuya, sai Firaministan kasar ya bayar da umarnin a kama wanda ya kai masa hari tare da daukan nauyin biyan kudin duba lafiyar Abubakar (lokacin da aka kai shi asibiti).

Tuni gwamnatin kasar Krygyzstan tura wanda ya kai wa Abubakar hari gidan yari.

An binne gawar Abubakar a birnin Bishkek a ranar 5 ga watan Yuli bisa tsarin addinin Musulunci.

A magana ta karshe da suka yi, Amina ta ce, "mun yi magana ta karshe 'yan mintuna kadan kafin a kashe shi. Mu na magana a waya, sai na ji katsam ya ce min 'ina zuwa'. Ban sake jin maganarsa ba, sai kawai labarin mutuwarsa na ji."

Iyalin Abubakar, da suka hada da matarsa da 'yan uwa, na neman gwamnatin Najeriya ta nema musu hakkin dansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel