An kara yi wa alhazan jihar Zamfara ragin kudin kujerar Hajji

An kara yi wa alhazan jihar Zamfara ragin kudin kujerar Hajji

Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCOM) ta ce maniyyata daga jihar Zamfara sun kara samun ragin kudin da yawansu ya kai Riyal 200 daga kudin kujerar Hajji na shekarar nan da suka biya.

Fatima Sanda Usara, shugabar sashen hulda da jama'a a ofishin babban sakataren hukumar NAHCOM, ce ta bayyana hakan a cikin wani jawabi da ta fitar. Ta ce ragin ya samu ne biyo bayan sake cinikin kudin gidan da maniyyata daga jihar za su zauna yayin aikin Hajjin bana.

Adadin kudin da aka rage, wanda ya kama kudin Najeriya N16,492.08, ya mayar da kudin da maniyyatan jihar suka biya a Hajjin bana zuwa N1,896.57.

NAHCOM ta mika godiya ta musamman ga gwamnatin jihar Zamfara a karkashin jagorancin gwamna Mohammed Bello Matawalle bisa goyon bayan da ta bayar da kuma rawar da ta taka wajen samar wa alhazan jihar ragin kudin muhalli. Hukumar ta kara da cewa hakan zai bawa maniyayyata daga jihar damar samun rarar kudi.

DUBA WANNAN: 'Yan arewa sun cika da murna da farinciki bayan Buhari ya yi wa Fulani makiyaya albishir mai dadi

Hukumar ta jinjina wa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Zamfara bisa juriyar da ta nuna wajen bawa maniyyata daga jihar karfin gwuiwa da kuma sauke nauyin da ke kan ta duk da irin kalubalen tsaro da ake fuskanta a jiharsu.

NAHCOM ta shaida wa maniyyata daga Zamfara cewa su tuntubi ofishin jin dadin alhazai na jiharsu domin karbar kudin da aka rage musu.

Kazalika, ta bawa wadanda suka riga suka sauka a kasar Saudiyya tabbacin cewa za a biya su rarar kudin da aka rage.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng