Amfani guda 10 da gwaza da ganyansa ke yi jikin da adam
Masana sun bukaci jama’a da su dunga yawan cin gwaza domin cewa yana dauke da sinadarai masu matukar amfani a jikin dan adam.
Bincike ya kuma nuna cewa ganyen gwaza na dauke da sinadarin kawar da cututtuka da suka hada da makanta, daji, hawan jini, da sauran su.
Ana iya sarrafa wannan abinci ta hanyar daffa shi ko kuma ayi miya da ganyen domin amfana daga gare shi.
A yankin arewacin Najeriya kuwa akan dafa gwaza domin a ci shi haka nan, ko da manja ko man gyada ko kuma miya.
KU KARANTA KUMA: Muhammadu Buhari ya ba yan Super Eagles tabbacin samun alawus dinsu kwanan nan
Ga wasu daga cikin amfanin da gwaza ke yi a jikin dan adam a kasa:
1. Ganyen gwaza na dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ wanda ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka.
2. Gwaza nab a mutum kariya daga kamuwa da cutar daji kowace iri.
3. Har ila yau gwaza na kare dan adam daga kamuwa da cutar sigari.
4. Yana taimakawa wajen nika abinci, kawar da ciwon ciki sannan da hana yawan yin bahaya.
5. Yana ƙara ƙarfin jijiyoyin jiki.
6. Yana dauke da sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin ƙashi.
7. Gayen gwaza na kere mutum daga kamuwa da hawan jinni.
8. Ganyen na dauke da sinadarin ‘Folate’ wanda ke inganta girman dan dake ciki sannan da hana mace mai ciki kamuwa da hawan jini.
9. Ta'ammali da gwaza na inganta maniyi a jikin maza.
10. Yana kara jini a jiki musamman ga yara kananan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng