Rudani: Dan sanda ya yi mutuwar ban mamaki ana saura sati biyu ya angonce

Rudani: Dan sanda ya yi mutuwar ban mamaki ana saura sati biyu ya angonce

Iyalin wani jami'in dan sanda a kasar Ghana mai shekaru 42, kofral James Yaw Appiah, sun bayyana shakkunsu a kan yanayin mutuwarsa yayin da ya ke kan aiki.

An samu gawar Appiah wanda aka fi kira da 'Antoa Cupers' a cikin rumfarsa ta aiki a kusa da asibitin gwamnatai na Bawku inda aka tura shi ya yi aiki.

A cewar iyalinsa, an gano cewa ya yi magana ta karshe a wayarsa ta hannu da Lady Prempeh, wata 'yar uwarsa mai rera wakokin yabo irin na addini, a ranar 4 ga watan Yuli da misalin karfe 2:30 na dare kafin daga bisani a samu gawarsa bayan wasu sa'o'i kalilan.

Wani babban wa a wurin marigayin, Dakta Nana Kusi Appiah Osraman, ya shaida wa wani gidan radiyon FM a Kumasi cewa rundunar 'yan sanda na son boye gaskiyar sanadin mutuwarsa ta hanyar kin sakin gawarsa ga danginsa. Ya yi zargin cewa rundunar 'yan sanda ta boye gawar Appiah a dakin ajiye gawa don jikinsa ya rube a kasa ganin wata shaida da za ta nuna cewa kashe shi aka yi.

DUBA WANNAN: Matasa sun fara aikin tsaftace mahaukata da ke gararamba a titunan garin Kaduna

Kazalika, ya zargi kwamandan 'yan sanda na yankin, DCOP Ampofo Duku, da hannu a cikin kisan Appiah, tare da bayyana cewa Marigayin ya taba fada masa cewa kwamandan na yi masa barazana a kan wata magana da ya ke da masaniya a kai, wacce kuma kwamandan ba ya son ta fita waje.

Dangin mamacin sun ce har yanzu an hana su ganin gawarsa, sati guda bayan mutuwarsa.

Kafin mutuwarsa, marigayin, mai 'ya'ya biyu, na shirin angonce wa a karo na biyu a cikin makonni biyu masu zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel