Za a fara jigilan Mahajjatan Najeriya daga Madina zuwa Makka a yau

Za a fara jigilan Mahajjatan Najeriya daga Madina zuwa Makka a yau

Hukumar da ke kula da jigilan alhazan Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa daga yau Alhamis, 18 ga watan Yuli, za ta fara jigilan mahajjatan kasar daga Madina zuwa Makka.

Jami’in NAHCON da ke kula da mahajjatan kasara a Madina, Alhaji Ahmad Maigari ya bayyana wa manema labarai a Madina a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli cewa hukumar ta ba wata kamfani mai suna Hafil kwangilar diban mahajjata 35,000 daga Madina zuwa Makka.

Hakazalika yace za a fara aikin jigilar mahajjatan ne da Alhazai 3,801 daga jihohin Katsina da Legas.

Yace motocin zamani da za a yi amfani dasu wajen aikin jigila na da kayayyakin more rayuwa kamar wifi, bandaki, na'urar sanyaya wuri a kuma firiji domin jin dadin mahajjatan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, hukumar kula da Alhazai ta jihar Legas ta gama wadanda za su sauke farali a wannan shekara. Mun samu labari cewa yanzu haka an sauke Maniyyata fiye da 2,000 na jihar a kasar Saudiyya.

An tattaro cewa kawo yanzu babu Maniyyacin jihar Legas da ya rage a gida bayan da sahun jrgin karshe ya ajiye Maniyyatan a kasa mai tsarki. Jirage 5 ne su ka yi jigilar Mahajjatan jihar Legas su 2, 100 na wannan shekara.

KU KARANTA KUMA: Yan iska sun far ma ayarin wani basaraken Yarbawa kan rigimar fili

An soma daukar sahun farin ne a ranar 10 ga wannan wata, yayin da a ka kammala dibar Maniyyatan dazu nan.

A ranar Talata, 16 ga Watan nan ne jirgin karshe ya sauke mutanen Legas har cikin Birnin Madina a cikin kasar Saudiyya inji Amirul Hajj na Legas na bana, Dr. Abdul Hakeem Abdullateef.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng