Buhari ya kabance da Sanata Lawan da Gbajabiamila a fadar Villa
A ranar Laraba 17 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan da kuma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a fadar Villa dake Abuja.
Shugabannin majalisun tarayyar biyu sun iso fadar shugaban kasa da misalin karfe 3.30 na Yammacin Laraba kamar yadda jaridar The Nation ta bayar da shaida.
A yayin da ganawar ke ci gaba da gudana a tsakanin masu riko da madafan iko na kasar, har ila yau shugaban kasa Buhari bai mikawa majalisar dattawa sunayen sabbin ministocin gwamnatin sa ba a wa'adin ta na biyu domin tantacewa.
Ko shakka babu a na ci gaba da kirdadon jerin sunayen wadanda sabuwar majalisar shugaban kasa Buhari za ta kunsa yayin da a yanzu ya kasance kusan kwanaki 50 da karbar rantsuwa ta wa'adin gwamnatin sa na biyu da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.
KARANTA KUMA: Rushewar Gini: Buhari ya jajantawa al'ummar jihar Filato
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar dattawan ta Najeriya na shirye-shiryen aiwatar da babban taro na mu-duka domin tattauna batutuwa kan harkokin rashin tsaro masu ci gaba da ciwa kasar nan tuwo a kwarya.
A wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, a yau Laraba shugaban kasa Buhari ya yi ganawar sirri da shugaban bankin kungiyar kasashen Yammacin Afirka, Bashir Mamman Ifo, a cikin fadar sa ta Villa dake birnin Abuja.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng