Irin wadannan wasikun na Obasanjo su ka jefa sa kurkuku Inji Tanko Yakassai

Irin wadannan wasikun na Obasanjo su ka jefa sa kurkuku Inji Tanko Yakassai

Daya daga cikin manyan Dattawan Arewa wanda su ka kafa kungiyar nan ta Arewa Consultative Forum (ACF), ya yi magana a game da wasikar da tsohon shugaban Olusegun Obasanjo ya yi.

Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa irin wadannan wasiku da Obasanjo ya saba fitarwa dabi’ar sa ce ta rashin kishin kasa. Yakasai ya bayyana wannan ne a Kano jiya, 15 ga Watan Yuli, 2019.

Yakasai ya fadawa Manema labarai cewa wannan wasika da Obasanjo ya rubutawa Buhari ta na iya jawo tashin hankali a kasar nan. A cewar Dattijon, son-kai ne ya ke sa Obasanjo wannan rubutu.

“Aikin da Janar Obasanjo ya ke yi, ba komai bane sai kokarin kawo tashin hankali a kasar nan idan irin wadannan kalamai da sako na kiyayya su na yawo .“ Inji Tanko Yakasai.

KU KARANTA: Wata kungiya ta nemi a yi wuf a cafke Obasanjo a Najeriya

A cewar Yakasai, irin wannan wasika da Obasanjo ya rubuta ne ya jawo masa shiga gidan yari a lokacin Janar Sani Abacha. Yakasai ya ce duk babu kishin kasa a rubuce-rubucen shugaban.

Alhaji Yakasai ya ya fahimci cewa manyan sojojin kasar nan kullum su na cikin fada ne da junansu ko da kuwa sun yi ritaya. Dattijon ya ce ba wannan karo ba ne farau wajen Obasanjo.

“Obasanjo ya yi wannan lokacin Ibrahim Badamasi Babangida, haka lokacin mulkin Sani Abacha har a ka zarge sa da shirin kifar da gwamnati.” Yakasai ya ce har yau wadannan wasiku na nan.

Babban Dattijon yace a baya Obasanjo ya aika wasika ga shugabanni irin Abdussalami da Jonathan da shi Buhari a baya inda ya ce bai ga wani abin a zo a gani a cikin abin da Obasanjo ya fadan ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel