Siyasar Kano: Abdulmumin Jibrin ya yi kaca-kaca da Abdullahi Abbas

Siyasar Kano: Abdulmumin Jibrin ya yi kaca-kaca da Abdullahi Abbas

Rikicin cikin gidan da a ke fama da shi tsakanin wasu bangarori na jam’iyyar APC mai mulki ya kai wani hali a jihar Kano inda har ta kai an fito ana maidawa juna kalamai a bainar jama’a.

Honarabul Abdulmumin Jibrin mai wakiltar Mazabar Kiru da Bebeji a majalisar tarayya ya fito ya zargi shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas da kawowa APC matsala a jihar.

Abdulmumin Jibrin ya yi watsi da zargin da a ke yi masa na cewa ya yi wa jam’iyya zagon-kasa inda ya ce Alhaji Abdullahi Abbas ne za a zarga da laifin shiryawa APC makarkashiya a 2019.

A wani faifai da ya shigo hannun Legit.ng Hausa, Jibrin ya yi barazanar tona asirin abubuwan da su ka faru a APC a zaben 2019 a dalilin yadda shugaban na APC ya ke jagorantar jam’iyyar ta su.

Jibrin ya yi kaca-kaca da shugaban na APC inda ya ce a dalilinsa ne jam’iyyar ta sha kasa a duk wuraren da ta rasa kuma har ta kai a ka yi kunnen doki a wajen zaben gwamnan Kano a bana.

KU KARANTA: Abba Gida-Gida zai gabatar da shaidu sama da 300 a Kotu

A cewar Hon. Abdulmumin Jibrin, gwamna Abdullahi Ganduje ya na da Masoya, amma irin su Abdullahi Abbas ne su ka jawowa tafiyar APC bakin-jini har zaben gwamna ya kai wani zagayen.

‘Dan majalisar ya kara jaddada mubaya’ar sa da cewa ya na tare da gwamna Abdullahi Ganduje dari-bisa-dari a Kano kamar yadda ya ke goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a sama.

Sai dai babban ‘dan majalisar ya nuna cewa shugaban APC na Kano, ba zai iya masa wata barazana ba domin kuwa asali ma su ne su kayi kutun-kutun wajen ganin an sake nada shi.

Jibrin ya ce yayin da gwamna ya ke faman yi wa jama’a aiki, babu abin da shugaban APC na jihar ya ke kokarin yi sai hada sa rikici da al’umma har ya ke cewa Abbas din ba zai canza halinsa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel