2023: An fara kai wa Osinbajo da Tinubu hari tun kafin a buga gangar siyasa

2023: An fara kai wa Osinbajo da Tinubu hari tun kafin a buga gangar siyasa

Da alamu an fara kai wa Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, da kuma babban jigon jam’iyyar APC watau Asiwaju Bola Tinubu da shirin yakin neman zaben 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa yanzu haka wasu manyan ‘yan siyasan kasar sun fara kitsa sharri iri-iri domin ganin yadda za a hana mulki komawa yankin Kudancin Najeriya a zabe mai zuwa.

Kamar yadda rahotannin su ka nuna, wani ‘Dan siyasan Arewa da ke zama a Kaduna ya fara kokarin tado wasu bincike a kan Asiwaju Bola Tinubu domin a rage masa kima a idanun jama’a.

Wannan ‘dan siyasa da rahoto bai nuna sunansa ba, ya soma bankado da binciken da a ke yi a kan Bola Tinubu ta wani Kamfani mai suna Alpha Beta Consulting Limited da a ke zargi da laifi.

Ana zargin kamfanin Alpha Beta Consulting Limited da laifin satar wasu kudi har Naira biliyan 100. ‘Yan adawa su na amfani da wannan zargi wajen hurawa Bola Tinubu na APC wutar siyasa.

KU KARANTA: Buhari ya ci kasuwa a bikin yaye Sojoji da a aka yi a Kaduna

Rahoton ya ce yanzu har an sheka Birnin Dubai a kasar waje an bugo wasu hotuna domin batawa wadannan manyan ‘yan siyasa suna kamar yadda PDP ta kitsawa APC sharri a lokacin zaben 2019.

Wani ‘dan siyasar ya bayyanawa jaridar cewa:

“Shiri ne na lissafin 2023 inda wasu a cikin APC da PDP ke kokarin ganin bayan takarar Yemi Osinbajo da Bola Tinubu. A na kokarin nunawa Duniya cewa Osinbanjo da Tinubu barayin gwamnati ne.”

Majiyar ta ce:

“Bayan kokarin raba Buhari da mataimakinsa da kuma Asiwaju Tinubu, wasu na kokarin ganin mulki bai koma Kudu a 2023 ba saboda burin siyasar su. Tinubu ne su ke gani zai zama cikas” Inji sa.

Daga cikin shirin shi ne a wargaza APC kafin 2023 domin a rusa takarar wadannan ‘yan siyasa idan an gaza hada su fada da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sunan yaki da Barayin kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel