Kai jama’a: Wata mata ta kona mijinta saboda zai mata kishiya a jihar Kano

Kai jama’a: Wata mata ta kona mijinta saboda zai mata kishiya a jihar Kano

Labari da muke samu daga shafin Rariya ya nuna cewa wata matar aure ta watsa ma mijinta rowan zafi saboda zai kara aure a jihar Kano.

Lamarin ya cika da wani malamin makarantar Firamare ne a Dambata wanda aka ambata da suna, Mallam Aliyu Ibrahim Fayan-fayan, inda a daran ranar Alhamis yana kwance sai matarsa ta tafasa ruwan zafi kuma ta kwara masa ruwan zafi a gabansa.

A bangaren shi Mallam Aliyu Ibrahim ya ce shi dai ya san ya fadawa Matarsa cewar zai kara aure, har ma ya bata kudade domin taje tayi siyayya irin kayan fadar kishiya da take so, sai dai kuma yace tun lokacin da ya fada mata ba su sami matsala da ita ba har take gaya masa cewar su zasu je su hado kayan ma.

Ya kara da cewa ko a ranar lamarin zai faru lokacin da zai je cikin garin Dambatta sai da ta bashi sakon siyayya ya yi mata, “ina kwance bayan Nagama jin taskar labarai to har na fita na siyo musu nama suka ci dama na tarar da ita tana dafa ruwan zafi naje na kwanta Kawai sai naji ta kwara min ruwan zafi kamar yadda kuka ganin shi,” Inji mijin.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bayar da belin uba mai shekara 60 da ya lalata yarsa mai shekara 8

Ya kara da cewa, “dan kurum nace zanyi karayin aure ne shiya sa, 'yan uwana duk sun san zanyi aure, amma har yanzu ban san inda take ba, domin lokacin da abin ya faru wani makwabcina ne ya taimakeni ya kawoni nan Asibitin inda nake kwance."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel