Yau Kotu za ta yanke hukunci a tuhumar da ake yi ma shugaba Buhari

Yau Kotu za ta yanke hukunci a tuhumar da ake yi ma shugaba Buhari

-Yau juma’a 12 ga watan Yuli 2019, kotu za ta yanke hukunci game da can-cantar tsayawar shugaba Buhari takarar

-Kalu Kalu da Labaran Isma’il Da Hassy El-Kuris sun tunkari kotun daukaka kara in da suka bukace ta da ta sauya hukuncin da babbar kotun gwamnatin tarayya tayi akan tuhumar da suke yi wa shugaba Buhari cewa bai can-canta tsayawa takara ba.

Yau juma’a 12 ga watan Yuli 2019, kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a tuhumar da ake yi ma shugaba Buhari akan can-cantarshi ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

A ranar 8 ga watan Yuli 2019, alkalai uku na kotun daukaka karar da Jastis Atinuke Akomolafe ke jagoranta sun sanaya ranar da za su yanke hukunci bayan da suka gama sauraron mahawara tsakanin lauyoyin masu shari’ar.

Kalu Kalu da Labaran Isma’il Da Hassy El-Kuris sun tunkari kotun daukaka kara in da suka bukace ta da ta sauya hukuncin da babbar kotun gwamnatin tarayya tayi akan tuhumar da suke yi wa shugaba Buhari cewa bai can-canta tsayawa takara ba.

A zaman da akayi na karshe a kotun, lauyan masu daukaka kara, Ukpai Ukairo ya bayyana cewa shugaba Buhari bashi da cikakken ilimin da zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa.

KARANTA WANNAN: Gwamnan Jigawa yayi magana da kakkausar murya akan dakatar da shirin Ruga

A cewarshi, babau takardun shaidar karatu da ake bukata a katin takarar shugaba Buhari mai namba CF001 da ya mika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) don a tantance shi.

A sabida haka Ukpairo ya bukaci kotun da ta amince da karar da suka daukaka, ta sauya hukuncin babbar kotun gwamnatin tarayya saboda ba ayi adalci ba a shari’ar.

Da yake maida martani, Lauyan shugaba Buhari, Abdullahi Abubakar, ya bayyana wa kotun cewa lokacin da doka ta bayar na a shigar da kara ya wuce, a sabida haka ya bukaci kotun da ta amince da hukuncin da babbar kotun gwamnatin tarayya tayi akan cewa masu tuhuma ba su bi dokar da ta bada lokacin shigar da kara ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel