Yan bindiga sun sake garkuwa da mutane 3 a yankin Abaji

Yan bindiga sun sake garkuwa da mutane 3 a yankin Abaji

Bayan kwana hudu da yin garkuwa da wani mai suna Ekene, yan bindiga sun sake garkuwa da mutane uku a kauyen Nuku da ke yankin Abaji.

Wani mazaunin kauyen wanda bai so a bayyana asalinsa ba yace lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 11:30 na dare a lokacin da yan bindigan suka kai hari kauyen suka kuma tafi da mutane uku.

Yace an sace Amos Takura da Micah Takura, kannen tshon sakataren karamar hukumar, Sule Takura tare da Shekwolo Anyinu, wani ma’akacin hukumar sufuri na birnin tarayyamai ritaya.

A cewar shi, yan bindigan sun shigo garin ne ta cikin daji inda suka fasa kofofin gidajen wadanda suka sace.

Basaraken Abaji kuma shugaban sarakunan babban birnin tarayya, Alhaji Adamu Baba Yunusa ya gayyaci dukkan shuwagabannin kabilu zuwa fadarsa a jiya Alhamis.

Alhaji Yunusa, yayin da yake jawabi ga shuwagabannin, ya bayyana damuwarsa akan lamarin garkuwa da mutane, ya bayyana cewa lamarin rashin tsaro a hukumar ya tilasta manoma barin harkan noma.

Yayi kira ga dukkan shuwagabannin kauyukan da sauran shuwagabannin kabilun yankin da su tabbatar da cewa sun kawo rahoto akan duk wani da ake zargi ga hukumomin tsaro a yankin.

KU KARANTA KUMA: Yan Abuja sun ba gwamnatin tarayya awa 48 ta kawo karshen zanga-zangar yan shi’a

Har ila yau, shugaban yankin hukumar Abaji, Alhaji Abdulrahman Ajiya, wanda sakataren hukumar ya wakilta, Alhaji Kamal Adamu Shuaibu ya bukaci shuwagabannin da su tabbatar da cewa sun goya ma jami’an tsaro baya tare da mika musu bayanai da zai taimaka wajen magantce lamarin garkuwa da mutane a yankin.

Shugaban yayi kira ga iyaye da su kula da yaransu da kuma irin abokai da suke hulda dasu, yayin da yake gargadin cewa duk mutumin da aka kama da dangantaka da masu garkuwa mutane zai fuskanci hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel