Abinda yasa na shiga kungiyar tsafi - Dalibi mai shekaru 14

Abinda yasa na shiga kungiyar tsafi - Dalibi mai shekaru 14

Wani dalibin karamar makarantar sakandire, Christopher Anthony, ya bayyana cewa ya shiga kungiyar tsafi ne domin yakar wasu makiyansa.

Sannan ya kara da cewa ya shiga kungiyar matsafan domin kare kansa daga cin zali a makaranta.

Matashin matsafin ya ce ya na zaune ne a kauyen mutum daya da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Ya amsa laifin cewa shi mamba ne a kungiyar matsafa yayin da rundunar 'yan sanda ta yi bajakolinsa a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Bola Longe, ya yi kira ga iyaye da masu rikon yara da su yi kokarin sauke nauyin da ke kan su ta hanyar bawa yara tarbiyya da sa ido a kan al'amuransu, musamman yaran da ke karatu a makarantun sakandire da gaba da sakandire.

DUBA WANNAN: Wani asibiti a Kaduna ya koka bisa yadda 'yan sanda ke yawan kai musu gawar mutane su jibge

Kazalika ya gargadi 'yan kungiyar matsafa da sauran 'yan ta'adda da su canja hali saboda rundunar 'yan sanda ba za ta taba daga kafa wajen tabbatar da ganin cewa ta raba jihar da matsafa ba.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta yi bajakolin mambobin kungiyar asiri wadanda mafi yawansu daliban makarantar sakandire ne a karamar hukumar Karu da ke jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel