Amfanin ruwan abarba guda 5 a jikin dan Adam
Abarba wani nau’i ne na kayan marmari ne mai matukar amfani a jikin dan adam. Ruwansa na taimakawa sosai wajen magance wasu laluri a jikin dan adam idan har zai lazumci shan sa.
Yana dauke da wasu sinadarai masu kara lafiya da kuzari a jikin mutum.
Ga wasu daga cikin amfaninsa:
1. Ruwan abarba na taimakawa wajen rage kiba
Kamar yadda muka sani mutane na wannan zamani na gudun kiba sosai, don haka idan aka samu ruwan abarba zai taimaka sosai a kan haka don ya na dauke da sinadarin thiamine wanda ke karawa jiki karfi wajen sarrafawa da narka ‘carbohydrate’ wanda shine kan gaba wajen saka jikin mutum tara teba. Cin abarka kan taimaka sosai saboda abarba na dauke da sinadarin fiber wanda ke taimakawa matuka wajen daidaita sigan cikin jinni dan Adam.
2. Yakar makoko
Abarba na dauke da sinadarin ‘iodine’ wanda ke taimakawa matuka wajen yakar makoko, da sauran cututtuka.
3. Kwarin kashi da lafiyar hakora
Abarba na dauke da sinadarin ‘potassium’, wanda ke taimakawa wajen lafiyar kasha, sannan kuma potassium na taimakawa matuka wajen lafiyar hakora sannan kuma ci ko shan ruwanta na taimakawa dadashi sosai.
4. Lafiyar Idanu
Binciken masana ya nuna cewa shan abarba na taimakawa idanu sosai sannan kuma yana taimakawa sosai wajen karfin gani ga mutanenda suka manyanta sakamakondimbin sinadarin ‘beta-carotene’ da ke ciki.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya amince da raba wa manyan makarantun Najeriya biliyan N5 domin gudanar da bincike
5. Abarba na taimakawa wajen saurin warkewa daga ciwo
Cin abarba zai taimaka matuka gaya wajen saurin warkewa daga ciwo, sinadaren da ke cikin abarba na taimakawa wajen saurin kawarda kumburi, zafi da konewa.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng