Dalilin goyon bayan masu Madigo da Luwadi yasa ba zan ziyarci Saudiyya ba – Nicki Minaj

Dalilin goyon bayan masu Madigo da Luwadi yasa ba zan ziyarci Saudiyya ba – Nicki Minaj

Fitacciyar mawakiyar nan ta turanci, Nicki Minaj, ta bayyana cewa sabanin sanarwar da aka yi a mako da ya gabata, ba za ta ziyarci kasar Saudiyya ba.

Da farko dai an tattaro cewa Minaj zata yi wasa ne a filin wasa na Sarki Abdullah da ke Jedda kafin ta canja shawarar rashin halartan chasun.

Babban dalilin da ya sa Mawakiyar canja shawarar duk da gayyatar ta da kasar Saudiyya ta yi mata shine don goyon bayan kungiyoyin kare ‘yancin mata masu madigo da masu Luwadi da take yi, kuma gashi kasar Saudiyya ta haramta hakan.

Mutane da dama sun yi ta tofin Alla tsina ga wannan shiri na gwamnatin kasar Saudiyya cewa shirya irin wannan buki bai kamata a ce kasa kamar Saudiyya za ayi shi ba, inda ake zuwa aikin Hajji sannan kuma a wannan kasa ne Kabarin Annabin Tsira Mohammadu SAW yake ba wai kuma za a yi irin wannan tambadewa a ciki.

Masu shirya wannan buki sun ce ba za a siyar ko a sha giya ko muggan kwayoyi a wannan wurin rawa ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sake gagarumin zanga-zanga a Abuja, sun ce sun shirya mutuwa

Idan ba za a manta ba wasu daga cikin kawaye, da abokan Minaj sun yi ta ja mata kunne cewa kada ta ta tafi kasar casu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel