Na bar fim saboda zai raba ni da Musulunci – Jarumar fina-finan Indiya

Na bar fim saboda zai raba ni da Musulunci – Jarumar fina-finan Indiya

Shahararriyar jarumar kamfanin shiya fina-finan Indiya wato Boolywood, Zaira Wasim mai shekara 18 a duniya ta bayyana cewa za ta daina harkar fim saboda abin da ta kira da barazanar da sana’ar fim din ke haifarwa ga sha’anin addini.

An tattaro inda jarumar ke fadin cewa: “Tafiya ce mai matukar wahalar sha’ani; da na share lokaci mai tsawo ina yakar ruhina.”

Indiyawa sun yi ta mayar da martani akan labarin nata; inda da dama suka yi ta sukar dalilinta na barin harkar fina-finan.

Tauraron Misis Wasim a harkar fina-finan ya soma haskawa ne a shekarar 2016, lokacin da ta fito a wani fim mai suna Dangal, daya daga cikin fina-finan Indiya da suka yi tashe a baya-bayan nan.

Jarumar-wacce ta fito daga yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi, ta yi karin haske kan irin fadi-tashin da ta sha a masana’antar fina-finan, da kuma yadda hakan ya shafi dangantakarta da addininta na Islama.

KU KARANTA KUMA: Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

Abin da ta wallafa a shafin sada zumuntar, tuni ya yadu inda ya yi ta samun dubban sharhi da nuna so.

Jarumar ta bayyana cewa a yayinda ta fara nazari tare da fahimtar abunda ta sadaukar da lokacinta a kai; sai ta gano cewa lokaci yayi da ya kamata ta bude sabon shafi na rayuwa; sai kawai taji cewa lallai ta dace da masana'antar amma dai ba wurin zamanta bane.

Jarumar ta ce sana'ar fim na nisantata da mahaliccinta, inda tace tana fama da raunin imani da rashn kwanciya hankali, sakamakon nisantata da ubangiji da harkar ke yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel